Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bamu cafke Ali Kwara ba -‘Yan Sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta ce bata kama fitaccen mai farautar barayinnan Alhaji Ali Kwara ba, kamar yadda ake yadawa.

Sai dai rundunar ta ce ta cafke wani mutum mai suna Aliyu Muhammad wanda ake yiwa lakabi da “Ali Kwara”.

Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaidawa Freedom Radio cewa sun cafke Aliyu Muhammad mazaunin unguwar Diga dake karamar hukumar Kumbotso wanda ake yiwa lakabi da “Ali Kwara” bisa zargin aikata manyan laifukan da suka hadar da fashi da makami da garkuwa da mutane.

Hoton Ali Kwara na Bogi

Har ila yau yana cikin gaggan ‘yan fashin da suka addabi dajin Falgore tun shekaru hudu da suka gabata.

Kazalika an sameshi sanye da kayan sojoji da kuma bindigogi kirar AK47 guda biyu da kuma kunshin harsashin bindinga har sinki biyu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!