Connect with us

Labarai

Ban san yawan mutanen da bidiyoyina ya taimaka wa ba wajen sauya rayuwarsu- MK Tecnic

Published

on

Fitaccen mai ƙirƙirar Fasaha a kafafen sada zumunta, Mutari Hamidu, wanda aka fi sani da MK Tecnic, ya ce har yanzu bai san adadin mutanen da bidiyoyinsa suka yi tasiri a rayuwarsu ba, amma saƙonnin da yake samu daga masu kallonsa na ƙarfafa masa gwiwar ci gaba da samar da bidiyoyin ilimantarwa.

MK Tecnic ya bayyana cewa tun bayan da ya fara karkata zuwa wallafa bidiyoyin da ke ɗauke da darussan rayuwa da saƙonnin ƙarfafa kyawawan ɗabi’u, yana ci gaba da karɓar saƙonni daga masu kallo da ke bayyana yadda abubuwan da yake wallafawa suka taimaka musu wajen sauya tunaninsu ko ɗaukar wasu matakai masu kyau.

A cewarsa, manufarsa tun farko ita ce ya yi amfani da kafafen sada zumunta wajen samar da abun ciki da zai kasance mai amfani ga al’umma, ba nishaɗi kaɗai ba.

“Ban san adadin mutanen da bidiyoyina suka taimaka wajen sauya rayuwarsu ba. Amma duk lokacin da wani ya rubuto min cewa ya koyi wani darasi ko ya gyara wani hali saboda wani bidiyo na, hakan yana ƙara mini ƙwarin gwiwar ci gaba da wannan tafiya,” in ji MK Tecnic.

Ya ƙara da cewa babban burinsa shi ne ya ci gaba da samar da bidiyoyin da za su zaburar da mutane su rungumi kyawawan ɗabi’u, su kasance masu tunani mai kyau, kuma su yi amfani da kafafen sada zumunta wajen amfana da kansu da al’umma.

Wasu daga cikin masu bibiyar ayyukansa sun bayyana cewa sabon salon da ya runguma ya sa bidiyoyinsa suka zama abin kallo tare da zama abin koyo, inda ake samun darussa masu amfani a cikin salon gabatarwa mai sauƙin fahimta.

MK Tecnic ya ce zai ci gaba da amfani da tasirin da yake da shi a kafafen sada zumunta wajen samar da abun ciki da ke ƙarfafa ilimantarwa, wayar da kai da kuma gina kyawawan dabi’u a tsakanin masu kallonsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!