Connect with us

Labarai

Saleem Top: Matashin ɗan Kano da ke amfani da TikTok wajen yaɗa sakonnin Addini

Published

on

Wani matashi daga jihar Kano mai suna Saleem Top na ci gaba da daukar hankalin dubban mutane a kafafen sada zumunta saboda irin salon da yake amfani da shi wajen kirkirar Islamic contents masu ilmantarwa.

Saleem Top, wanda ake kallonsa a matsayin daya daga cikin fitattun Islamic content creators a Arewa Najeriya, ya samu karbuwa sosai musamman a TikTok da Facebook, inda mabiyansa ke karuwa a kullum.

A cewar masu bibiyar harkokin social media, Saleem Top ya shahara ne saboda yadda yake hada ilmantarwa, nasiha da fadakarwa cikin sauki da fahimta ga matasa.

Matashin ya bayyana cewa tun farko burinsa shi ne anfani da social media wajen yada sakonni masu anfani ga al’umma da kuma karfafa gwiwar matasa su anfani da intanet ta hanya mai kyau.

“Na fara content creation ne domin in yada sakonni masu anfani da ilmantarwa musamman ga matasa,” in ji Saleem Top.

Masoya da mabiyansa na yabawa yadda yake amfani da harshen Hausa cikin sauki wajen gabatar da sakonninsa, lamarin da ya taimaka wajen samun karbuwa sosai a Arewa Najeriya.

Baya ga TikTok, Saleem Top na daga cikin matasan Arewa da suka yi fice sosai a Facebook, inda rahotanni ke nuna cewa yana daga cikin wadanda suka fi samun mabiya a yankin Arewa Najeriya.

Wasu daga cikin mabiyansa sun bayyana cewa contents dinsa na taimakawa wajen ilmantarwa, fadakarwa da kuma kawo sauyi mai kyau ga matasa masu anfani da social media.

Yayin da yake ci gaba da samun karbuwa, mutane da dama suna kallonsa a matsayin daya daga cikin sabbin fuskar digital media influencers daga Arewa Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!