Connect with us

Labarai

ICC ta tsige mai gabatar da ƙara da jagoranci bayar da sammacin kama Netanyahu

Published

on

Ƙasashen da ke mambobin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) sun kaɗa kuri’ar amincewa da tsige babban mai gabatar da ƙara na kotun, Karim Khan.

Ana zargin lauyan ɗan Birtaniya mai shekara 56 da dabi’ar da ba ta dace ba – a kan wata karamar ma’aikaciyar kotun – zargin da ya musanta.

Wakiliyar BBC ta ce wannan zargi ya fara bayyana ne a shekara ta 2024, cewa ya ci zarafi ta lalata na karamar abokiyar aikinsa.

Karim Khan ya jagoranci kotun tsawon shekara biyar, wanda a cikin wannan lokaci, kotun ta bayar da sammacin kama mutane da dama da suka haɗa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, da wasu jami’an ƙungiyar Hamas, da Shugaban Rasha Vladimir Putin, da tsohon shugaban Philippines Rodrigo Duterte.

Tsige Khan na zuwa ne a wani lokaci da kotun ta duniya ke fuskantar ƙalubale, sakamakon matakan Amurka na neman raunana ikonta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!