Connect with us

Labarai

Bangarorin siyasar Libya da ke takaddama sun sanya hannu kan yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya

Published

on

Bangarorin siyasar Libya da ke takaddama sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta goyi baya, wadda ake ganin za ta share fagen gudanar da zabukan kasa da aka dade ana jinkirta su.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Tripoli, a hedikwatar tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Libya, yayin da shugabar tawagar, Hanna Tetteh, ta halarta.

 

Yarjejeniyar ta tanadi gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki cikin watanni 24, matukar an samu gwamnati guda da kuma dunkulewar hukumomin kasar.

Libya ta shafe shekaru tana fama da rikicin siyasa tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasar, Muammar Gaddafi, a shekarar 2011.

 

A halin yanzu akwai gwamnatoci biyu da ke fafutukar iko da kasar, wato gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a Tripoli karkashin Firaminista Abdulhamid Dbeibah, da kuma wata gwamnati a gabashin kasar da ke samun goyon bayan kwamandan soji Khalifa Haftar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!