Connect with us

Labarai

Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe sama da biliyan 37 a tafiye-tafiye cikin shekaru 3

Published

on

Fadar Shugaban Ƙasa ta kashe sama da Naira biliyan 37 wajen tafiye-tafiyen cikin gida da na ƙasashen waje cikin shekaru uku.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar bayanan da dandalin GovSpend, mai bibiyar yadda ake kashe kuɗin gwamnati a kasar nan ne ya fitar da kididdigar.

 

Rahoton ya ce tafiye-tafiyen sun shafi wanda Shugaban Ƙasa ke yi na zirga-zirga daga watan Yunin 2023 zuwa Afrilun 2026.

 

Ko a ranar Lahadi data gabata Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake barin Najeriya zuwa Turai domin hutun shekara na tsawon makonni uku.

 

Hakan ya zo ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo daga hutun makonni biyu.

 

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu zai dawo Najeriya bayan hutun aiki domin shiga cikin shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!