Labarai
Sokoto: Yan Bindiga sun hallaka manoma 8 tare da raunata 5 a kauyen Ghandi

Akalla manoma takwas ne aka kashe, yayin da wasu biyar suka jikkata sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Ghandi da ke ƙaramar hukumar Rabah ta Jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce maharan sun shiga yankin ne da misalin ƙarfe uku na ranar Lahadi, inda suka buɗe wa manoman wuta, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa rundunar na tattara bayanai game da abin da ya faru.
Wani mazaunin yankin ya ce ana zargin harin da ɗaukar fansa ne, bayan da jami’an tsaro suka kashe wasu daga cikin ‘yan ƙungiyar ‘yan bindigar a yayin wasu samame da suka gudanar a yankin a kwanakin baya.
You must be logged in to post a comment Login