Labarai
Bankin CBN ya bawa manoma bashi a Kano
Kungiyar manoman masara da sarrafata da kuma kasuwancinta ta kasa wato Maize Growers Processors and marketers Association of Nigeria (MAGPAMAN) ta jaddada kudirin ta na ci gaba da inganta harkokin noma musamman noman masara a kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa reshen jihar Kano, Alhaji Yusuf Ado Kibiya, ne ya bayyana hakan yayin da yake mika tallafin bashi na irin shuka da babban bankin kasa CBN ya samar ga manoman masara a nan jihar Kano.
Alhaji Yusuf Ado kibiya ya kuma ce “A domin haka manoman da suka amfana da tallafin noman ya zama wajibi su yi amfani dashi ta hanyar da ta dace musamman wajen ganin an inganta harkokin samar da abinci a kasar nan”.
Covid: Sama da mutum 500,000 ne suka mutu a fadin duniya
Shirin Bunkasa Noma da Kiwo na jiha zai fara yiwa dabbobi Allura ta Rigakafi
Yayin da yake nasa jawabin kakakin kungiyar ta (MAGPAMAN) a nan Kano, Malam Sani Haruna Limawa, kira ya yi ga manoma mata kan su shigo cikin tsarin na bayar da tallafin domin suma su ci gajiyar shirin na babban bankin na kasa CBN.
Wasu daga cikin manoman da suka amfana da shirin sun bayyana farin cikin su, “inda suka ce zasuyi amfani da tallafin irin shukar ta hanyar data dace”.
A kalla sama da manoman masara dubu biyar da dari bakwai da sittin da hudu ne zasu amfana da tallafin kayan noman da suka hadar da irin shuka dana masara da maganin kwari da kuma taki.
You must be logged in to post a comment Login