Connect with us

Labarai

Covid: Shugaba Buhari ya sabunta dokar kulle

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tsawaita dokar zaman gida dole, zuwa mako hudu.

Dokar za ta fara aiki ne da tsakar daren ranar Talata, wanda ya yi dai-dai da 30 ga watan Yunin 2020.

A wata tattaunawa da ya yi da Freedom Radio, mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen sada zumunta wato, Bashir Ahmad ya ce dokar za ta rika aiki ne daga misalin karfe shida na safe zuwa 10 na dare.

Wanna ya zo ne a dai-dai lokacin shugaba Buhari ke jagorantar zaman tattaunawa ta musamman da shugabannin kwamitin kar-ta kwana kan yaki da annobar Covid-19 na fadar shugaban kasa.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da ministan Osagie Ehanire da shugaban hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC Dakta Chikwe Ihekweazu.

Ana sa ran wa’adin dokar takaita zirga-zirgar za ta kare a ranar 27 ga atan Yulin 2020.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!