Kasuwanci
Bankin Masana’antu zai tara Yuro miliyan 750 daga kasuwannin bashi

Bankin bunkasa masana’antu na Najeriya (BoI) ya bayyana shirin tara kudade Yuro miliyan 750 daga kasuwannin bashi na duniya a bana.
Za dai ayi amfani da kudaden ne wajen bayar da bashi ga kamfanonin da su samu nakasu sakamakon annobar Corona.
Shugaban Bankin, Olukayode Pitan tuni aka samu kwararru a harkokin kudi don ba da shawarwari kan batun.
You must be logged in to post a comment Login