Labaran Wasanni
Barcelona ta yi wa Messi murna zagayowar ranar haihuwa
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta aike wa Lionel Messi da sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
A yau Alhamis 24 ga watan Yunin 2021 ne, Messi ya cika shekaru 34 a duniya.
Kawo yanzu dai dan wasan bai san makomarsa ba a kungiyar, yayin da kwantiraginsa ke shirin karewa a karshen wannan watan na Yuni da muke ciki.
Messi ya yi yunkurin barin Barcelona a shekarar 2019 inda kungiyar ta gindaya mashi wasu ka’idoji da zai cika matukar yana bukatar ficewa daga kungiyar, lamarin da ya janyo takaddama har ta kaiga zuwa kotu.
You must be logged in to post a comment Login