Connect with us

Labaran Wasanni

Lauyan Barcelona na yunkurin dakatar da cinikin Lionel Messi

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta shigar da korafi a gaban hukumar tarayyar Turai a yankurin dakatar da Lionel Messi daga ficewa daga kungiyar.

Lauyan dake wakiltar Barcelona ne ya gabatar da korafin yana kalubalantar damar da PSG ke da ita na ka’idar kudaden da zata iya kashewa wajen sayan dan wasa bai kai darajar na Barcelona.

A yau Litinin ne 9 ga watan Augusta PSG ke dakon zuwan Messi don ci gaba da taka leda a kungiyar.

Messi ya tabbatar da ficewarsa daga Barcelona bayan da ya shafe shekaru 21 a kungiyar, yayin da yake bankwana a ranar Lahadi 8 ga watan Augustan 2021.

Ya ce, a shirye yake da ya rage albashinsa da kaso 50 domin ya ci gaba da zama a kungiyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!