Labarai
Barista MB Shehu ya raba fiye da Naira miliyan 4 tallafin jarin Sana’o’i
Kimanin mata da matasa 43 yan asalin Mazaɓun ƴan Mata gabas da Fagge A sun amfana da tallafin Naira Miliyan huɗu da dubu dari hudu daga ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Fagge Muhammad Bello shehu domin yin amfani da kudin wajen bunƙasa sana’o’insu.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin da suka haɗa da mutane 16 da kowannensu ya rabauta da Naira dubu ɗari biyu, sai mutum 7 da suka samu dubu ɗari-ɗari da kuma mutum 20 da ɗan majalisar ya bai wa Naira dubu Hamsin-hamsin, sun karbi tsabar kuɗin ne yayin taron rabon tallafin wata-wata da ɗan majalisar tarayyar na Fagge Barista MB Shehu ya ƙaddamar a jiya Juma’a.
Da ya ke jawabi bayan raba tallafin, Barista Muhammad Bello Shehu, ya ce, wannan somin taɓi ne a cikin irin matakan da ya ɗauka don taimaka al’ummar mazaɓar tasa.
Ɗan majalisar tarayyar mai wakiltar Fagge Barista MB Shehu, ya kuma ja hankalin wadanda suka rabauta da tallafin kuɗin da su tabbatar sun yi amfani da su yadda ya dace domin rage musu irin halin matsin tattalin arziki da ake ciki.
Barista MB shehu, ya bayyana cewa, 16 daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin za a ba su Naira 200,000 kowanne, yayin da 7 daga cikinsu za su samu Naira 100,000 kowannen su, mutane 20 kuma kowanne su zai samu N50,000.
Ya kara da cewa shirin tallafin wanda aka kaddamar a ranar Juma’a a mazaɓu biyu na Fagge A da Yanmata Gabas zai ci gaba da gudana duk wata.
Dan majalisar ya bayyana cewa ya raba kudaden ne ga wadanda suka ci gajiyar shirin daga cikin albashin da yake karba na wata-wata, wanda a cewar sa, za a ci gaba da daukar mazaɓu guda biyu a kowane wata har zuwa watan Disamba na wannan shekara.
“Wannan ba ya daga cikin aiyukan mazaɓu, tallafi ne daga cikin albashina na wata-wata a matsayina na dan majalisa naga ya dace na tallafa wa waɗanda suka yi aiki tukuru tare da tallafa mana wajen samun nasarar zabenmu a cewarsa.
“Sun cancanci fiye da wannan, saboda wadannan mutanen su ne suka sha rana suka sha wuya, kuma sun fuskanci cin zarafi daga yan adawa kala-kala har Allah ya bamu nasara don haka ya zama wajibi mu tallafa musu”.
MB Shehu ya kuma ce ya tanadi ayyuka da dama ga al’ummar karamar hukumar Fagge, inda ya bayyana cewa zai fito da managartan tsare-tsare na taimaka wa al’ummar sa, ta yaddada sauran ‘yan majalisu za su rika yin koyi da shin nan da ‘yan watanni masu zuwa.
A nasu ɓangaren, wasu cikin waɗanda suka samu tallafin, sun bayyana farin cikinsu tare da shan alwashin yin amfani da kuɗin domin su ma su zama masu cin gashin kansu.
Tun da farko a nasa jawabin, wani na hannun damar majalisar, Mustapha Isa, ya ce MB Shehu yana da kishin mutanensa don haka yake gudanar da ayyukan da za su inganta rayuwar al’ummarsa.
You must be logged in to post a comment Login