Labarai
Bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru da Naira tiriliyan 20.8 a shekaru 6 na mulkin Buhari
Ofishin kula da basuka na ƙasa (DMO), ya ce, bashin da ake bin ƙasar nan ya ƙaru da aƙalla naira tiriliyan 20.8 tsakanin watan Yuli na shekarar 2015 zuwa Disamban shekarar da ta gabata ta 2020.
A cewar rahoton ofishin na DMO a wannan lokaci Najeriya ta biya bashin naira biliyan 10.26
Kundin bayanan da ofishin kula da basuka na ƙasa ya fitar ya nuna cewa a ƙarshen watan Yuni na shekarar 2015 bashin da ake bin Najeriya ya tsaya ne akan naira tiriliyan 12.12
Yayin da a ranar 31 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2020 jimillar bashin da ake bin ƙasar nan ya kai naira tiriliyan 32.92.
Wanda hakan ya nuna cewa tsakanin wannan lokaci na watanni 66 bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru da aƙalla Naira tiriliyan 20.8
You must be logged in to post a comment Login