Labaran Wasanni
Basketball: zamu lashe gasar Afrobasket da za’ai a kasar Ruwanda-Mike Brown

Mai horas da ‘yan wasan kwallon Kwando na Najeriya, D’TIGERS, Mike Brown, ya ce yana fatan Najeriya za ta lashe gasar cin kofin kwallon Kwando ta Afrobasket ta bana.
A yau ne dai 24 ga watan Agustan da muke ciki za’a fara gudanar da gasar ta wannan shekara, inda za’a karkareta a ranar 5 ga watan Satumba mai kamawa.
Za dai a gudanar da gasar a babban filin wasa na Kigali dake kasar Ruwanda.
Najeriya na cikin rukunin C da kasar Mali da Kenya da kuma kasar Ivory Coast.
A gobe laraba dai 25 ga watan na Augusta Najeriya za ta fafata da kasar Mali a wasan farko da zatai na rukuni kafin daga bisani ta kara da kasar Kenya da kuma Ivory Coast.
You must be logged in to post a comment Login