Kiwon Lafiya
Baturen zabe sanata ta gabashin jihar Ogun ya ce ba’a kammala zaben sanata ba
Baturen zabe na mazabar sanata ta gabashin jihar Ogun Farfesa Chris Nwoka ya bayyana cewa ba’a kamamla zaben sanata a yankin ba.
A yayin da ake tattara sakamakon zaben na kananan hukumomin 9 na yankin jam’iyyar APC ta sami kuri’un dubu tamanin da hudu da dari tara da Ashirin da tara yayin da jam’iyyar PDP kuwa ta sami kuri’u Dubu Tamanin da biyu da dari hudu da Hamsin da bakwai.
Farfesa Chris Nwoka ana gab da za’a sanar da cewa dan takarar jam’iyyar APC sanata Mustapha Olaleken ne ya lashe zaben sai magoya bayan abokin takarar sa na jam’iyyar PDP Sosanwo Ayoola suka tada hargitsi.
Haka zalika kuma an soke zabe a mazabo 10 dake yankin karamar hukumar Ijebu ta gabas dake jihar Ogun, bayan da aka sami banmbaci mai yawa na yawan masu kada kuri’u da kuma yawan al’ummar dake yankin.