Connect with us

Labarai

Bauchi: Mutane biyu sun rasu yayin da takwas suka jikkata sakamakon rikicin Inkil da Bujinji

Published

on

Mutum biyu sun rasu yayin da wasu takwas suka jikkata sakamakon sabon rikicin da ya ɓarke tsakanin matasan ƙauyukan Inkil da Bujinji a Jihar Bauchi.

 

Rahotanni sun bayyana cewar, ana zargin matasan ƙauyen Inkil da kai harin ramuwar gayya kan Bujinji sakamakon wata tsohuwar taƙaddama da ke tsakanin al’ummomin biyu, Lamarin da ya faru da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Lahadi.

 

Bayan samun kiran neman agaji, jami’an ’yansanda sun garzaya wajen tare da kai waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Ƙwararru na Jihar Bauchi domin samun kulawa.

 

Daga baya, likitoci sun tabbatar da mutuwar mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Al-Amin Mohammad Aliyu da Jibir Shuaibu, dukkansu mazauna ƙauyen Inkil.

 

An tura jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana sake ɓarkewar rikicin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!