Addini
Bayan ficewar ƙalarawi daga kwamitin masallaci: majalisar dokoki ta hana ci gaba da gini a masallacin waje da ke Fagge
Majalisar dokokin jihar Kano ta ba da umarnin dakatar da duk wasu gine-ginen shaguna da ake yi a jikin masallacin Juma’a na Abdullahi Bayero da ke Fagge.
Majalisar ta bada umarnin ne a zamanta na ranar Talata, biyo bayan ƙudurin gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ƴan gurasa ya gabatar.
Ɗan majalisar ya bayyana takaicinsa kan yadda aka gine da dama ta hanyar samar da shagunan kasuwanci daga cikin filin makarantar, don haka ya buƙaci majalisar ta ɗauki matakan da suka dace.
Ƙudurin nasa dai, ya janyo tafka muhawara a tsakanin mambobin majalisar inda daga bisani ta cimma matsayar bada umarnin dakatar da gine-ginen.
Haka kuma majalisar ƙarƙashin shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim, ta kafa kwamitin mutane tara da za su binciki lamarin tun daga tushe kuma tare da gabatar da rahoton kwamitin cikin makonni biyu.
Mambobin kwamitin sune; Muhammad Uba Gurjiya mai wakiltar ƙaramar hukumar Bunkure a matsayin Shugaba.
Mambobin kuwa sune: Sunusi Usman Bataiya, Magaji Dahiru Zarewa Nuhu Abdullahi Achika, Lawan Hussaini Chediyar ƴan gurasa Abubakar Dalladi Isa Kademi Muhd Tukur Sale Ahmed Marke yayin da Mataimakin Daraktan Ayyukan Shari’a a matsayin Sakataren kwamitin.
Wannan dai ya biyo bayan ficewar Shiekh Tijjani Bala Kalarawi daga kwamitin amintattu na masallacin sakamakon yadda ake gini a masallacin kuma babu wani bayani da aka yi masa.
You must be logged in to post a comment Login