Ƙetare
Baza mu dawo da Shugaban da muka hambarar ba- Sojin Nijar
Babban mai shiga tsakani na ƙungiyar raya tattalin arziƙin yammacin Afrika ECOWAS domin sassanta rikicin Nijar, Janar
Abdulsalami Abubakar ya ce ‘sojojin da suka hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum sun ce a shirye suke su tattauna da ƙungiyar ECOWAS amma ba za su mayar da tsohon shugaban ƙasar a kan kujerarsa ba’.
‘Kungiyar ECOWAS ta ɗin dai ta bukaci sojojin dake mulkin da su sauka daga kan mulki ba tare da ɓata lokaci ba sannan su mayar da Bazoum a kan mulki ko kuma a ɗauki matakin soji a kan su’.
Cikin wata hira ta musamman da kafar yaɗa labarai ta BBC, Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa ‘tattaunawar da suka yi da shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ta buɗe ƙofar samun maslaha a matsalar da ake ciki’.
Rahoton: Yusuf Sulaiman Ahmad
You must be logged in to post a comment Login