Labaran Kano
Bazoum ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Nijar
Da yammacin Talatar nan ne hukumar zaɓe ta mai zaman kanta ta jamhuriyar Nijar CENI ta bayyana sakamakon ƙarshe na zaben shugaban ƙasa zagaye na biyu da aka gudanar a ranar lahadin nan da ta gabata.
Ɗan takarar jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki Mala. Bazoum Mohamed shi ne ya yi nasarar lashe zaben.
Shugaban hukumar zaɓen Maître Issaka Souna ce ta sanar da a shalkwatar CENI ɗin da ke a babban birnin Yamai.
Bazoum dai ya yi nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri’u 2,501,459 adadin da ya kai sama da kaso 55 da cikin 100.
Labarai Masu Alaka:
Nijar: Bazoum ya kama hanyar lashe zaɓe
Taron ECOWAS : Buhari zai gana da takwarorin sa a Jamhuriyyar Nijar
Shi kuma abokin hamayyarsa na jam’iyyar RDR Tchanji Alhaji Mahaman Ousman ya samu ƙuri’u 1,985,756 adadin da ya kai kaso 44 da ƴan kak cikin ɗari.
A tsarin mulkin ƙasar dai duk wanda ya yi nasarar lashe sama da kaso 50 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa shi ne ya lashe zabe ko da kuwa a zagaye farko ne, haka abin yake a zagaye na biyu.
You must be logged in to post a comment Login