Connect with us

Labarai

Benue: Mutane 7 sun mutu sakamakon harin yan bindiga

Published

on

Akalla mutane 7 ne suka rasa rayukan su sakamakon wani hari da yan bindiga suka kai a yankin karamar hukumar Logo a jihar Benue. 

 

Shugaba karamar hukumar yankin , Chief Joseph Anawah ya tabbatar da faruwar lamarin a ganawarsa da manema labarai a makurdi inda yace yan bindigar sun kashe mutane 7 tare da jikkata 4.

 

Wasu Shaidun gani da ido sun shaida cewa harin da akai a ranar Lahadi ya jikkata wasu da dama baya ga asarar rayuka Inda sukace Yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe daya na rana akan babura dauke da makamai inda suka budewa mutanen yankin wuta 

 

Shugaban karamar hukumar yankin na  Logo, Chief Joseph Anawah,ya ce an garzaya da wadanda suka jikkata asibiti domin basu taimakon gaggawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!