Labarai
Za a gurfanar da mutumin da ake zargi da kai hari a fadar gwamnatin Amurka

Nan gaba kadan a yau Litinin za a gurfanar da mutumin da ake zargi da kutsawa wajen wata liyafar cin abinci domin kai hari ga Shugaban Amurka, Donald Trump.
Za a tuhumi Cole Tomas, mai shekara 31 a duniya, dan Los Angeles, da laifin kai hari ga jami’in gwamnatin tarayya da kuma amfani da bindiga yayin aikata laifin.
Ana zargin ya buɗe wuta ne a kusa da wurin binciken jami’an tsaro, lamarin da ya tilasta fitar da Shugaba Trump daga wurin cikin gaggawa.
Jami’an tsaro sun ce an samu wani sakon email da maharin ya aikawawa ‘yan uwansa mintuna kaɗan kafin ƙaddamar da harin, inda a ciki yake bayani a kan shirin sa na kai hari kan jami’an gwamnatin Mista Trump din.
You must be logged in to post a comment Login