Connect with us

Labarai

Rundunar soji ta kai ziyara gidan iyalan matashin da dan NYSC da aka kashe

Published

on

Rundunar sojin Najeriya, ta kai ziyara gidan iyalan Abdulsamad Jamiu, matashin dan hidimar kasa NYSC da aka kashe shi a Abuja.

 

Hukumar, ta bayyana cewa, ana gudanar da bincike a kan lamarin.

 

Ziyarar, ta biyo bayan kin amincewar iyalan da bayanin farko na sojoji cewa Jamiu ya mutu ne sakamakon harbin musayar wuta da ‘yan fashi da ya ritsa da shi.

 

Iyalan mamacin sun ce hujjoji sun nuna cewa, ba a yi wata musayar wuta da wau ‘yan ta’adda ba, in da suka zargin jami’an soji da cewa, sun shiga harabar gidan sannan suka harbe shi ta kofar dakinsa har sau biyu, lamarin da ya kai ga mutuwarsa nan ta ke. 

 

A yayin ziyarar, wakilan sojin sun jajanta wa iyalan tare da cewa za a binciki jami’an da abin ya shafa kuma za a dauki mataki. 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!