Connect with us

Labaran Kano

Bikin Kirsimeti: Za mu gudanar da tsaftar muhalli na ƙarshen wata – Dakta Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano za ta gudanar da ɗuban tsaftar muhalli a gobe Asabar.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya tabbatar da hakan ta cikin wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radio a ranar Juma’a.

Ya ce, kamar kowanne ƙarshen wata za a gudanar da tsaftar muhalli na ƙarshen watan Disamba duk da cewa ana tsaka da gudanar da bikin Kirsimeti.

“Muna sane da cewa gobe akwai shagulgulan bikin Kirsimeti amma ba zai hana mu gudanar da duban tsaftar muhalli ba”.

Ya ci gaba da cewa “Duban tsaftar muhalli na gobe na musamman ne domin zai mayar da hankali wajen duban tsaftar banɗakunan kasuwanni da tashoshi sannan ba zai hana kowa yayi zirga-zirga ba”.

Dakta Getso ya kuma ce, a ranar juma’a mai zuwa kuma za a gudanar da tsaftar muhalli na kasuwanni kamar kowanne wata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!