Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bikin ranar mata na bana ya bambanta da na baya- Gwamnatin Kaduna

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce, bikin ranar mata ta duniya na bana ya bambanta da sauran bukukuwan da aka gudanar a shekarun baya.

Kwamishiniyar jin kai da walwalar jama’a ta jihar Hajia Rabi Salisu ce ta bayyana haka a zantawarta da Freedom Radio Kaduna.

Ta ce, kamar yadda taken taron na bana yake, ƙarfafa wa mata gwiwa domin su shigo a dama dasu a bangarori na rayuwa, hakan ta sa gwamnatin jihar Kaduna a karkashin ma’aikatar ta suka shirya taron bitar da za’a ƙara wayar da kan mata da kuma basu damar nuna fasahohin sana’oi da suke dashi.

Haka kuma, a cewar ta akwai dokoki da gwamnatin jihar Kaduna ta samar domin kare ƴancin mata da kananan yara a faɗin jihar Kaduna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!