Labarai
Bikin sabuwar shekara: Ba za mu amince da aikata baɗala ba a matsayin murna – Ibn Sina
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta gargaɗi matasa da su guji wuce gona da iri a yayin bukukuwan sabuwar shekara.
Babban kwamandan hukumar Shiekh Harun Muhammad Sani Ibn Suna ne ya bayyana hakan a wani sauƙon murya da ya aikowa Freedom Radio.
Ibn Sina ya ce, suna sane da yadda matasa ke amfani da bukukuwan sabuwar shekara suna aikata baɗala da sunan murna.
“Haƙƙin iyaye ne ku san ina yaranku za su je, wane abu suke aikatawa da sunan murna, domin kuwa a shekarar bara mun ga yadda matasa suka riƙa baɗala da shaye shaye a ƙwaryar birni lamarin da ya sanya suka riƙa jikkata kan su” a cewar Ibn Sina.
“To mu Hisba ba za mu yarda da irin wannan ɗabi’u ba, don haka za mu baza jami’an mu lungu da sako don hanawa”.
Shiekh Harun Ibn Sina ya buƙaci iyaye su tsawatar da yaransu kan aikata munanan dabi’u.
You must be logged in to post a comment Login