Labaran Kano
Bikin zagayowar ranar haihuwa: Kwankwaso ya buɗe gidan gyaran hali a Kano
Tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ƙaddamar da gidan gyaran hali a Jido da ke ƙaramar hukumar dawakin kudu a kano.
Injiniya Rabi’u Kwankwaso ya ce an ƙaddamar da cibiyar ne domin magance matsalolin tsaro da kuma gyara tarbiyyar matasa.
“Yadda yanzu ake yawan samun matasa na mu’amala da miyagun kwayoyi da aikata miyagun laifuka, babu abinda ya rage face a samar da guraren gyaran hali da tarbiyya a fadin jihar Kano”.
Siyasa ba da gaba ba: Ganduje ya taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwar sa
Kwankwason ya ƙara da cewa “Muna fatan al’umma za su bada haɗin kai wajen magance wannan matsala da matasa suke fama da ita domin kawar da matsalar ta sheye-shaye ƙwacen waya da sauran laifuka a jihar.
“Yanzu haka cibiyar ta fara aiki domin kuwa akwai mutane da aka fara kulawa da su a cikin ta” a cewar Kwankwaso.
Wannan jawabin dai na zuwa ne a wani ɓangare na bikin cikar tsohon gwamnan shekara 65 a duniya.
You must be logged in to post a comment Login