Labarai
Bincike: An sayar da makaranta saboda biyan kuɗin fansa
An sayar da wani bangare na makarantar islamiyya ta Tanko Salihu da ke Tegina a karamar hukumar Rafi a Jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa, an sayar da makarantar ne don tara Naira miliyan 50 kudin fansar ɗaliban makarantar a karo na biyu na dalibai 136 da ƴan bindiga suka sace.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa wannan ta biyo bayan koken da iyayen ɗaliban ke yi na rashin dawowar yaran su gida daga hannun ƴan bindigar.
Kimanin kwanaki 79 kenan ɗaliban suka shafe a hannun a masu garkuwa da su, wanda hakan ya sanya iyayen su suka fara sayar da wani bangare na makarantar don tara kudin.
Labarai masu alaka:
Da ɗumi-ɗumi – Ƴan bindiga sun sako kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa a farko sun biya maharan kudin fansa da ya kai naira miliyan 50 don sakin yaran.
Koken iyayin dai ya biyo bayan yadda a baya-bayan nan ƴan bindiga suka sace kwamishinan yaɗa labaran jihar, kuma suka sako shi a ƙankanin lokaci.
You must be logged in to post a comment Login