Labarai
Boko Haram ta taɓa naɗa Buhari a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar sulhu- Jonathan

Tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa, ƴan ta’addar Boko Haram, sun taɓa naɗa tsohon Shugaban Najeriya marigayi Muhammadu Buhari a matsayin wakilinsu domin shiga tattaunawar sulhu da Gwamnatin Tarayya.
Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin kaddamar da littafin “Scars” da tsohon Hafsan Soja, Janar Lucky Irabor mai ritaya ya rubuta.
A cewar Jonathan, gwamnatinsa ta kafa kwamitoci daban-daban domin lalubo hanyar tattaunawa da ’yan Boko Haram, inda a wani lokaci cikin irin waɗannan shirye-shirye, mayakan suka ambaci Buhari a matsayin mutumin da suke son ya jagoranci tattaunawar.
Ya ƙara da cewa saboda haka, ya yi tunanin zai kasance da sauƙi ga Buhari lokacin da ya zama shugaban ƙasa ya tattauna da su har su mika wuya, amma lamarin yaƙin ya ci gaba da ɗaukar lokaci.
You must be logged in to post a comment Login