Kiwon Lafiya
Boko haram:sun kai hari kauyukan da kan iyakan jihohin Adamawa da Borno a jiya
Dagacin Duhu na jihar Adamwa Mohammed Sanusi ya ce mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kauyukan da ke kan iyakokin jihohin Adamawa da Borno da ya hada da Michika da Madagali a daren ranar Litinin da ya sanaya sukan kona gidaje saboda su yi jidon kayayyakin abinci ne.
Wasu mazauna yankin da suka boya da wanda suke tsire kan tsaunika sun shedawa manema labarai cewa a yayin kai harin ‘ya’yan kungiyar Boko Haram sun yi wa yara kanana da datijawa da kuma barasa lafiya da bindigogi.
Sai dai kawo yanzu hukumomin tsaro ba su bayyana irin asarar da aka tafka ba.
A cewar Malam Sanusi ya ce ‘yan tada kayar bayar sun dawo kauyukan ne domin daukar fansa, bayan da suka gaza yin katabus yayin kai harin da suka yi na karshe a yankunan Michika da Madagali kwanaki 7 ke nan, kasancewar rundunar sojan saman kasar nan ta maida martani.
Rahotanni sun bayyana cewar wannan shi ne hari na 3 da kungiyar Boko Haram din da kai wadannan kauyuka na Madagali da Michika a jihar Adamawa a cikin wata guda