Labarai
Borno: Yan sanda sun fara kamen ababen hawa marasa lamba

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Borno ta fara kamen motoci da sauran ababen hawa da ba su da lamba da kuma wadanda ke rufe lambobinsu.
Jaridar Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a jiya Laraba.
Daso Ya ce, matakin na daga cikin kokarin dakile laifuka, inganta tattara bayanan sirri da kuma hana masu aikata laifuka amfani da motocin da ba su da sahihiyar rajista.
Sanarwar ta ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Borno, Naziru Abdulmajid, ya bukaci masu ababen hawa su tabbatar da cewa motocinsu suna da sahihiyar lambar rajista.
Rundunar ta yi gargadin cewa wadanda ke amfani da lambobin da aka rufe ko aka sauya za su fuskanci hukuncin.
You must be logged in to post a comment Login