Connect with us

Labarai

Hukumar NCAA ta dakatar da lasisin kamfanin jirgin da ya sauka a titin mota

Published

on

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa, wato NCAA, ta dakatar da lasisin kamfanin da ke gudanar da wani jirgin sama mai zaman kansa bayan da jirgin ya sauka a kan titin mota a yankin Ogwashi-Uku da ke kusa da Asaba a Jihar Delta.

 

Mai magana da yawun hukumar, Michael Achimugu, ya ce rahotannin farko sun nuna cewa jirgin ya kasa sauka yadda ya kamata a Filin Jirgin Sama na Asaba da misalin ƙarfe 7:43 na safiyar Laraba, lamarin da ya sa matukin jirgin ya sake yunƙurin sauka kafin daga bisani jirgin ya sauka a wani titi da ke yankin.

 

Sai dai hukumar ta tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa ko ya samu munanan raunuka, domin duka fasinjojin da ma’aikatan jirgin sun fito lafiya daga cikin jirgin, sannan aka ɗauke su zuwa Asaba ta mota. 

 

NCAA ta ce ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin tare da ɗaukar matakan da suka dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!