Connect with us

Labarai

Kotun ta umarci INEC ta yi wa jam‘iyyar Access rajista

Published

on

Kotun tarayya ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC kan ta yi wa jam‘iyyar Access rajista.

 

Wata kotun tarayya wadda da ke zamanta a Abuja ce ta bayar da wannan umurnin, sannan ta umarci INEC ta ba jam’iyyar damar ƙarasa rajistarta.

 

Jagororin jam’iyyar Dr. Audu Bulama-Bukarti da Mevon Samuel su ne  suka maka INEC a kotu, bayan hukumar zaben ta ƙi amincewa da ita, inda ta kafa hujja da cewa tambarin jam’iyyar ya yi kama da tambarin wata jam’iyyar.

 

Da yake yanke hukunci, alƙalin kotun Mai shari’a Obiora Atuegwu Egwuatu na kotu mai lamba 11, ya ce hukumar ba ta da hurumin hakan, inda ya nanata cewa hukuncin ba daidai ba ne, kuma ya saɓa da shari’a kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tsara da kuma sashe na 79 na kundin zaɓe na shekarar  2022.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!