Labarai
Buɗe makarantu: Ministan ilimi ya kawo ziyara Kano
Ƙaramin ministan ilimi na ƙasa Mr. Chukwuemeka Nwajuba ya kawo ziyara fadar gwamnatin Kano a daren yau Asabar.
Ministan ya ce, ya kawo ziyarar ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen sake buɗe makarantu.
Ya ƙara da cewa, cikin abubuwan da ziyarar ta mayar da hankali bayan batun buɗe makarantun shi ne matakan kariyar da za a ɗauka domin kaucewa bazuwar cutar a tsakanin ɗalibai.
Da yake jawabi yayin ziyarar, a madadin gwamnan Kano, mataimakin sa Dr. Nasir Yusuf Gawuna ya ce, ya zama lallai a godewa gwamnatin tarayya bisa yadda ta ke, bin dukkan matakan da suka da ce, kafin sanya ranar sake buɗe makarantu.
Nasiru Gawuna ya ce, tuni jihar Kano ta yi nisa wajen horas da shugabannin makarantu da malamai kan yadda za a kare yaɗuwar cutar idan an buɗe makarantu.
Daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin Kano ke yi na buɗe makarantu tuni aka yi feshin magani a makarantun da ke faɗin jihar.
Wakiliyarmu ta fadar gwamnatin Kano Zahra’u Nasir ta rawaito cewa kwamishinan ilimi na jihar Kano Muhammad Sanusi Ƙiru yana daga cikin waɗanda suka karɓi tawagar ministan.
You must be logged in to post a comment Login