Manyan Labarai
Buhari Bai Damu Da Harkokin Lafiya Ba-Likitocin Yara
Daga Abdullahi Isa
Kungiyar likitoci ta kasa masu kula da cututtukan yara (PAN), ta soki lamirin gwamnatin tarayya game da rashin nuna halin ko in kula ga bangaren lafiya.
Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Augustine Omoigberele ne yayi wannan sukar, yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a nan Kano, a wani bangare na shirye-shiryen fara babban taronta na kasa.
Abinda ke ciwa mutane tuwo a kwarya a asibitin AKTH Kano
Ana zargin likita da sanadin mutuwar mara lafiya
‘‘Kungiyar PAN ta damu matuka game da kudaden da gwamnati ta ware ga bangaren lafiya a cikin kasafin kudin wannan shekarar, ko kadan wadannan kudaden ba za su dakile tarin matsalolin da ke addabar bangaren ba’’-Inji Farfesa Augustine.
Da ya ke karin haske kan batun, shugaban kwamitin shirya taron, Farfesa Mu’utasim Ibrahim, ya ce, wasu daga cikin bangarorin da kungiyar za ta tattauna yayin taron, sun hada da: nazartar bincike-bincike da masana suka gudanar kan cututtukan da ke addabar yara da kuma rashin abinci mai gina jiki tsakanin yaran kasar nan.
Farfesa Mu’utasim Ibrahim ya kara da cewa, taron wanda shine karo na hamsin da daya da kungiyar za ta gudanar zai kuma nemi hadin kan gwamnatin jihar Kano domin rika tura mambobin kungiyar zuwa yankunan karkara domin gudanar da ayyukan kula da lafiyar yara na wucin gadi.
A cewar sa, kungiyar, ta kuma horas da jami’an lafiya guda hamsin a yankin karamar hukumar Bichi da ke jihar ta Kano.