Kasuwanci
Buhari ga Atiku: Kafin na hau mulki ƴan Najeriya miliyan 30 ke fama da talauci
Fadar shugaban kasa ta soki kalaman da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya yi a baya-bayan nan wanda ya alakanta matsalar da kasar nan ke fuskanta a wannan lokaci da salon mulkin shugaba Buhari.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, kafin zuwan shugaba Buhari kan karagar mulki mutane sama da miliyan talatin ne ke fama da kangin talauci a Nigeria.
Femi Adesina ya kuma ce kididdigar da hukumar NBS ta fitar a baya-bayan nan da ke cewa, mutane miliyan ashirin da uku da dubu dari biyu ba su da aikin yi, ba sabon abu bane.
Adesina ya tabbatar da hakan ne ta cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na channels a jiya lahadi.
Da ya ke mai da martani kan tambayar da akai masa Adesina, ya ce, ‘‘idan za a iya tunawa kafin kama mulkin shugaba Buhari a shekarar 2015 a adadin al’umma da ba su da aikin yi a Nigeria, ya tasamma miliyan 30, kuma mafi yawancin su matasa ne’’.
You must be logged in to post a comment Login