Labarai
Buhari ga hafsoshin tsaro: Wajibi ne ku kawo karshen ‘ayyukan ‘yan ta’adda kafin faduwar daminar bana
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sabbin hafsoshin tsaron kasar nan da su yi duk me yiwuwa wajen kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a kasar nan kafin faduwan daminar bana.
A cewar-sa jami’an tsaron suna da wa’adin ‘yan makwanni ne kawai a gabansu da ya debar musu don dakile matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a yau juma’a lokacin da ya ke rantsarwa tare da kara girma ga sabbin manyan hafsoshin tsaron a fadar Asorok.
Shugaba Buhari ya ce yana fata kafin saukar daminar bana hafsoshin tsaron za su dakile matsalolin tsaro wanda hakan zai bai wa manoma damar komawa gonakinsu don samar da abinci ga kasa.
Muhammadu Buhari ya kuma bukace su da su bai wa hazikai daga cikin jami’ansu dama don su yi amfani da kwarewar da su ke da shi wajen fuskantar barazanar tsaro da ake fama da ita a wannan lokaci.
Manyan hafsoshin tsaron da aka karawa girma tare da rantsar da su sun hada da: babban hafsan tsaron kasar nan Janaral Lucky Irabor da babban hafsan sojin kasa laftanal Janar Ibrahim Attahiru, Vice Admiral Awwal Zubairu babban hafsan sojan ruwa da kuma Air Marshal Isiaka Amoo, babban hafsan sojin sama.
You must be logged in to post a comment Login