Labarai
Buhari ya amince a biya likitocin dake kan gaba a yaki da Corona hakokin su
Gwamnatin tarayya ta amince da biyan naira biliyan ashirin hakkokin likitoci da ma’aikatan lafiya dake gaba-gaba wajan yaki da cutar corona a fadin kasar nan.
Ministan lafiya Dr Olorunnimbe Mamora ya bayyana hakan ta cikin tattaunawa da akayi dashi a gidan talabijin na Channels a yau laraba.
Mamora ya yabawa likitoci da maaikatan lafiya dake gaba gaba wajan jajircewar su wajan yakar annobar cutar corona.
Ministan ya kara da cewa kimanin likitoci dubu goma sha shida suka ajiye aikin su sakamakon gwamnatin tarayya ta gaza wajan biyan hakkokin su wanda ya hada alausa alaus na inshore da yaki da cutar corona da kuma na horas da maaikatan lafiya da likitoci da sauran su.
Ya kara da cewa koda yake gwamnatin tarayya bata gayyace su taron tattauna matsalolin ba kafin sanarwar likitocin da maaikatan lafiya zasu tafi yajin aiki a fadin kasar.
Koda yake kungiyar likitoci masu neman kwarewa sun sanar da tafiya yajin aikin tun ranar litinin data gabata.
You must be logged in to post a comment Login