Labarai
Buhari ya amince da bukatar tattaunawa da kamfanin Twitter
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar tattaunawa da kamfanin Twitter ya bukata kan batun dakatar da ayyukan sa a Najeriya.
Shugaba Buhari ya bada umarnin hada wata tawaga da za ta hada da Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Mohammed wanda shi ne zai jagoranci tawagar don tattaunawa da kamfanin.
Cikin tawagar sun hada da ministan shari’a kuma Atoni Janar na kasa Abubakar Malami, da ministan sadarwar da bunkasa tattalin arziki Dr Isah Ali Ibrahim Pantami da kuma ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyema.
Sauran su ne: ministan ayyuka da gidaje BabaTunde Raji Fasola da kuma karamin ministan kwadago da samar da aikin yi Festus Keyamo, da sauran manyan ma’aikatan gwamnati.
Tuni dai kamfanin Twitter ya ce a shirye yake don tattaunawa da gwamnatin kan dakatar da shi daga ayyukan su a Najeriyar.
Dakatarwar dai ta biyo bayan goge wani rubutu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa.
You must be logged in to post a comment Login