Labarai
Buhari zai yi kokari wajen dai-daita farashin kayan masarufi a Najeriya
Shugaban kasa muhammadu Buhari ya ce zai yi iya bakin kokarin sa wajen ganin an dai daita farashin kayyakin masarufi da sukayi tashin gwarzaon zabi a fadin kasar nan.
Muhammad Buhari ya bayyana hakan ne a shafinsa na twita kan halin matsin rayuwa da al’ummar kasar nan suka tsince kansu a ciki dangane da tashin kayyakin masarufi.
Shugaba Buhari ya ce tashin kayayyakin masarufin ya biyo bayan annobar covid 19 da kuma ambaliyar ruwa da matsin tatalin ariziki da kasar ta samu kanta a ciki.
You must be logged in to post a comment Login