Kasuwanci
Buhari: Za a bude sabon kamfanin takin zamani
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a cikin watanni masu zuwa ne gwamnatin tarayya za ta kaddamar da sabon kamfanin sinadarin amoniya da kuma takin zamani da aka gina kan kudi sama da dala biliyan daya.
Wannan na cikin wata sanarwa da mashawarcin shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya fitar, inda ya ce Najeriya za ta gina masana’antar ce tare da hadin gwiwar kasar Morocco.
Adesina ya ce sabon kamfanin zai yi aiki tare da na Dangote da Indoroma, wadanda ke samar da sinadarin Urea da amoniya da sauran kayayyakin masana’antu.
Ya kara da cewa idan aka hada wadannan ayyuka tare da masana’antu safarar sinadarai 44 da ake da su ,to ko shakka babu Najeriya za ta zama cibiyar samar da takin zamani na yankin.
You must be logged in to post a comment Login