Labarai
Buhari zai yi titi daga Sokoto zuwa Nijar
Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da kudi naira biliyan ashirin da tara, na aikin kwangilar gina hanya daga Sokoto zuwa Jigawa ya zarce zuwa Jamhuriyyar Nijar.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ne ya sanar wa da manema labarai hakan jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta kasa wanda aka saba yi duk ranar Laraba da shugaba Muhammad Buhari, ke jagoranta a babban birnin tarayya Abuja.
Rahotanin sun bayyana cewar, a yayin zaman majalisar zartarwar an kwashe sama da awanni takwas ana gudanar da shi bisa jagorancin shugaban kasa da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo.
Labarai masu alaka:
APC zata daukaka kara kan shari’ar zaben gwamnan Sokoto
Ba muyi nadamar zabar Buhari ba -Izala
Babatunde Fashola, yace aikin za a faro shi ne daga yankin Belle da Kurdulla, dake ba kin iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar a bangaren na jihar Sokoto.
Fashola, ya kara da ce wa kamfanin kwangila na hadin gwiwar wasu kamfanunuwa guda biyu ne, za su gudanar da aikin akan kudi fiye da naira biliyan ashirin da tara.
Haka kuma, aikin titin yana da nisan kilo mita 46 kuma ana saran cewar, za’a kammala shi cikin watanni 24, masu zuwa nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login