Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

BUK ta horas da mutane kan yadda zasu rika sarrafa kudaden su

Published

on

Cibiyar nazarin harkokin bankuna da kudi a musulince ta jami’ar Bayero, ta ce da yawa daga cikin kudaden da mutane suke kashewa a wannan lokacin suna kashesu ne ta hanyar da bata daceba.

Daraktan cibiyar Farfesa Binta Tijjani Jibril ce ta bayyana hakan yayin taron horar da Ilimin harkokin kudi ga kungiyoyin makarantun addinin Musulunci da cibiyar ta gudanar yau a tsangayar koyar da ilimin shari’a dake jami’ar ta Bayero a nan Kano.

Farfesa Binta Tijjani Jibril ta kuma ce ya kamata mutane su koyi yadda za su dinga kashe kudaden su ta hanyar da ta dace ta yadda tattalin arzikin kasar nan zai bunkasa yadda ya kamata a hanyoyi da dama.

Ta kuma ce da yawa daga cikin mutanen kasar nan suna samun kudade a ayyukan da suke gudanarwa sai dai basu san irin hanyoyin da za su bi ba wajen kashe kudaden na su ta hanyar data dace.

Farfesa Binta Tijjani Jibril

Farfesa Binta ta kuma yi kira ga gwamnatocin kasar nan kan su dage wajen bunkasa ilimi a tsakanin al’umma ta yadda za su iya kashe kudaden su ta hanyar da ta dace.

Har ila yau ta kuma ja hankalin gwamnati wajen samar da ayyukan yi tsakanin al’ummar kasar nan, ta yadda za’a rage mutanen da basu da ayyukan yi.

Wasu daga cikin mutanan da suka halarci taron horarwar sun bayyana jindadin su, bisa yadda aka gudanar da laccar musamman yadda aka nuna musu yadda za su kashe kudaden su a tsarin addinin musulinci.

Masana harkokin kudi da dama ne suka halarci taron horarwar inda sukayi bayanai da dama kan yadda ya kamata mutune subi wajen kashe kudaden su.

Labarai masu alaka:

BUK: dalibai 300 sun sami tallafin karatu

Jami’ar Bayero ta bukaci mahukunta su cigaba da amfani da takardun SUKUK don ciyar da al’umma gaba

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!