Labarai
BUK ta sanya ranar Jarabawar Post UTME

Jami’ar Bayero da ke Kano ta sanar da ranakun Alhamis, juma’a da kuma Asabar,18, 19, 20 ga watan da muke ciki na Maris a matsayin ranakun da za a gudanar da jarabawar gwaji na dalibai da ke neman gurbin karatu a jami’ar wadanda suka rubuta jarabawar JAMB wato Post UTME.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da jami’ar ta fitar a jiya juma’a.
A cewar jami’ar, shafin website da za ayi rajistar jarabawar ta gwaji wato Aptitude Test za a rufeshi da karfe goma sha biyu na daren juma’a sha biyu ga wannan wata.
Saboda haka jami’ar ta bukaci dalibai da ke neman gurbi a jami’ar da su tabbata sun cire takardar shaidar shiga ajin rubuta jarabawar wato examination slip tsakanin ranakun Alhamis zuwa sha biyar ga watan Maris.
Sai dai jami’ar ta ce, za a iya ci gaba da fitar da takardar ta slip wato shaidar shiga ajin rubuta jarabawar har zuwa ranar Laraba 17 ga wata.
You must be logged in to post a comment Login