Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan filayen jiragen sama

Published

on

‘Yan bindiga sun kai hari rukunin gidajen jami’an hukumar kula da filayen jiragen saman kasar nan da ke garin Kaduna, inda suka sace mutane tara.

Rahotanni sun ce cikin wadanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su, har da iyalan wani gida su shida da wata matar aure da ‘ya’yanta biyu.

Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun samu nasarar shiga rukunin gidajen ma’aikatan filin jirgin saman ne ta titin sauka da tashin jirage da ke cikin filin jirgin.

Lamarin ya kuma faru ne da misalin karfe goma sha biyu da rabi na daren jiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!