Labarai
Buratai, Olonisakin, Ibas, Sadique sun ci kudin makamai – Monguno
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Manjo janar Babagana Monguno mai ritaya, ya ce, akwai wasu kudade da aka ware don sayo makamai da nufin yaki da ta’addanci, da su ka yi batan dabo zamanin manyan hafsoshin tsaro da suka gabata.
Manyan hafsoshin tsaron da ake zargi da cinye kudin makaman sun hada da: Janar Abayomi Olonisakin mai ritaya, tsohon babban hafsan tsaro, Laftanal janar Tukur Buratai, tsohon babban hafsan sojan kasa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas mai ritaya, tsohon babban hafsan sojan ruwa da kuma Air Marshal Sadique Abubakar, tsohon babban hafsan sojan sama.
A yayin wata zantawa da gidan radio BBC Hausa a yau juma’a, Manjo janar Babagana Monguno mai ritaya ya ce babu wanda ya san abin da ya faru da kudaden.
‘‘Tuni hankalin shugaban kasa ya karkata kan zargin kuma zai ba da umarni da a gudanar da bincike don gano inda kudaden suka makale’’ acewar Monguno.
Ya ce, manyan hafsoshin tsaro da suka gajesu sun tabbatar da cewa ba su ga inda makaman da tsofaffin manyan hafsoshin tsaron suka saya da kudaden ba.
A shekarar 2015 ne dai shugaba Buhari ya nadasu a matsayin manyan hafsoshin tsaro kafin daga bisani ya sauke su a watan Janairun wannan shekara.
You must be logged in to post a comment Login