Labarai
Bututun mai ya fashe a Legas
Al’ummar unguwannin Surulere, Ijegun da Ikotun da Egbeda da Abule Ado, da Okota sai Isheri da Olofin dana Festac Town, suna daga cikin unguwannin da hatsarin rushewar gidaje da kamawar wuta ta same su a safiyar yau sakamakon fashewar wani bututun mai a jihar Lagos da safiyar yau Lahadi.
Fashewar da aka tashi da ita da safiyar yau, ta haddasa asarar dukiyoyi da gidaje na miliyoyin nairori, wanda wasu al’ummar yankin da suke ganau suka shaida sai dai zuwa yanzu ba ayi asarar rai ba.
A rahoton da jaridar the Cable, ta fitar wani mazaunin unguwar Abule Ado , ya shaida musu cewar ya hango wata makaranta na ci da wuta ganga -ganga, ya yinda wani ganau din daga unguwar Egbeda, ya tabbatar da rushewar gine gine na makwabta, wanda yace ya gani Jim kadan bayan dawowar sa daga Coci a safiyar ta yau.
Zuwa yanzu dai da ake hada rahotanni ba ‘a tabbatar da makasudin da ya haddasa fashewar bututun ba.Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos (LASEMA) ta tabbatar da fashewar Bututun na mai a unguwar Abule Ado, dake karamar hukumar Amuwo Odofin ta jihar.
Hukumar kashe gobara ta kasa Fedaral Fire service , ta tabbatar da cewar tana aiki kafada da kafada da reshenta na unguwannin Badagry da Festac , don samun cikakken bayanin mai yake faruwa da matakan da za’a dauka ,kamar yadda ta sanar a shafin ta na Twitter.
All @Fedfireng Stations in Lagos have turned out to the scenes of explosion, except Festac, Ebute Metta and State house Fire trucks which are on Standby.
Our Surulere Fire truck is Stuck in the rubble, our Emergency truck is on the way to the scene of Fire to pull it out.— Federal Fire Service (@Fedfireng) March 15, 2020
You must be logged in to post a comment Login