Labaran Wasanni
Carlos Ponck: za mu yi duk me yiwuwa wajen lallasa Super Eagles
Dan wasan baya na kasar Cape Verde Carlos Ponck, ya ce za su yi duk mai yuwuwa wajen ganin sun doke kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagle a wasan da za su buga yau Talata 7 ga Satumbar 2021.
Ya ce burin kasar shine ganin ta yi nasara a gabaki dayan wasannin ta na gida, a wasan neman tikitin buga gasar cin kofin Duniya da za’a gudanar a kasar Qatar a shekara ta 2022.
Yan wasan Najeriya 9 ba za su buga wasan Cape Verde ba -Rohr
Kasar Cape Verde dai za ta fafata da Super Eagle yau a babban filin wasan ta mai suna, Stade Municipal Adérito Sena dake yankin Mindelo a kasar.
A jiya Litinin dai ‘yan wasan na Najeriya suka sauka a kasar ta Cape Verde ba tare da wasu daga cikin manyan ‘yan wasan ta ba 9 dake buga wasa a kasar Ingila.
Hakan ya biyo bayan ta kunkumin da hukumar kwallon kafar kasar Ingila ta sakakawa ‘yan wasan dake wasa a kasar na hana su shiga wasu kasashe dake fama da annobar Corona ciki kuwa harda kasar ta Cape Verde.
You must be logged in to post a comment Login