Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

World Cup 2022: Qatar za ta kaddamar da filayen wasanni 6 gabanin gasar

Published

on

Shekara guda kafin fara gasar cin kofin Duniya ta shekarar 2022 da za’a gudanar a kasar Qatar.

Hukumar kwallon kafa ta kasar za ta kaddamar da filayen wasanni 6 a watan Oktobar 2021 kafin fara gasar.

Bude filayen wasannin zai gudana a ranar 22 ga watan Oktobar da wasan karshe na gasar (Amir Cup) na kasar.

Qatar 2022: Kasar Masar ta sallami mai horar da ‘yan wasan ta

Filayen wasannin da suka hada da na Al-Thumama da na Khalifa International, sai kuma  Al Janoub da Education City da  Ahmad Bin Ali da kuma na Al-Bayt, filayen da tuni suka zama cikin shiri gabannin gasar ta  shekarar 2022.

Kungiyoyi biyu da suke buga gasar a kasar ta Qatar da su ka hada da  Al-Sadd da tsohon dan wasan Barcelona da kasar Sipaniya Xavi Hernandez  ke jagoranta da kuma kungiyar Al-Rayyan da dan kasar Faransa Laurent Blanc ke jagoranta sune za su buga wasan na karshe a gasar ta Amir Cup.

Filin wasa mai daukar mutane dubu 40,000 na Al-Thumama zai karbi bakuncin wasannin gasar har zuwa wasan dab dana kusa dana karshe.

Gasar cin kofin duniya a Qatar dai za ta gudana daga ranar 21 ga Nuwamba zuwa 18 ga Disambar shekarar 2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!