Labarai
CBN ta bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki naira biliyan 33 don sayo mitar wuta – NERC
Hukumar kula da al’amuran wutar lantarki ta kasa ta ce babban bankin kasa CBN ya bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki jimillar naira biliyan talatin da uku da miliyan dari hudu don sayo mitar wutar lantarki
A cewar hukumar ta NERC tun farko bankin na CBN ya yi alkwarin bai wa kamfanonin naira biliyan hamsin da tara da miliyan dari biyu wanda tuni ya saki sama da naira biliyan talatin da uku.
Shugaban hukumar Injiniya Sanusi Garba ne ya bayyana haka yayin zantawa da kwamitin kula da harkokin samar da wutar lantarki na majalisar dattijai jiya a Abuja.
Ya ce shirin wani bangare ne na kokarin gwamnati na samarwa gidaje miliyan daya mitar wutar lantarki tsakanin watan Oktobar shekarar da ta gabata da watan Afrilu wannan shekarar.
Ya ce tuni an sayo mita guda dubu dari hudu da uku kuma har an mika su ga kamfanonin samar da wutar lantarki.
You must be logged in to post a comment Login